16 Afirilu 2020 - 04:59
​Macron: Ina Da Tabbacin Cewa Putin Zai Amince Da Shirin Zaman Lafiya A Duniya

Shugaban kasar Faransa Emmanuel macron ya fadi yau cewa, zai tattauna da shugaba Putin na Rasha kan kiran da babban sakataren majalisar dinkin duniya ya yi, na dakatar da duk wasu tashe-tashen hankula a duniya.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Faransa Emmanuel macron ya fadi yau cewa, zai tattauna da shugaba Putin na Rasha kan kiran da babban sakataren majalisar dinkin duniya ya yi, na dakatar da duk wasu tashe-tashen hankula a duniya.

A zantawarsa da gidan radiyon Faransa a safiyar yau Laraba, Macron ya bayyana cewa; ya tattauna da shugabannin kasashen Amurka, China, da Firayi ministan Burtaniya kan aiwatar da shawarar da Antonio Guterres ya gabatar, a kan dakatar da duk wasu tashe-tashen hankula a duniya a cikin irin wannan yanayi na corona.

Macron ya ce yana da tabbaci kan cewa shugaba Putin zai amince da hakan, kuma da zaran ya amince, za a kira taron shugabannin kasashe masu kujeru na din-din-din a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, wato Rasha, China, Faransa, Amurka da kuma Burtaniya, domin su tattauna ta hanyar hoton bidiyo kan yadda za a aiwatar da shirin.




/129