13 Afirilu 2020 - 05:13
Za A Yi Musayar Fursunoni Tsakanin Hamas Da HKI

Majiyar Palasdinawa ta bayar da labari a yau Lahadi cewa, za a yi musayar fursunonin palasdinawa tsofaffi da kananan yara da suke a kurkukun hki da bayanan da za a bai wa ‘yan sahayoniyar akan fursunoninsu a Gaza.

(ABNA24.com) Majiyar Palasdinawa ta bayar da labari a yau Lahadi cewa, za a yi musayar fursunonin palasdinawa tsofaffi da kananan yara da suke a kurkukun hki da bayanan da za a bai wa ‘yan sahayoniyar akan fursunoninsu a Gaza.

Jaridar “Ha’aratz” ta HKI ta ambaci cewa kungiyar Hamas ce ta gabatar da shawarar a sako tsoffi da kananan yara fursunoni da su ke a gidajen kurkukun ‘yan sahayoniyar a matsayin share fagen yin musayar sauran fursunonin.

Sai dai jaridar ta ‘yan sahayoniyar ta ambato wata majiya daga cikin kurkukun wacce take cewa babu wata alalama da take nuni da cewa ana shirin yin musayar fursunoni.

A daya gefen HKI ta bukaci kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas akan ta saki Apraham Mansato a matsayin jin kai, sai dai hakan ba ta faru ba saboda yadda Masar mai shiga tsakani ta mayar da hankali wajen fada da cutar Corona.

Da akwai kananan yara 250 da su ke cikin gidajen kurkukun HKI, banda wadanda su ke zaman wucin gadi.



/129