(ABNA24.com) Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, dakarun sa kai na al’ummar kasar Iraki Hashd Al-sha’abi, sun bayar da sanarwar cewa, a jiya sun samu nasarar fatattakar wasu gungun mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a yankin Nahrain, da ke cikin lardin Dayali a gabashin birnin Bagadaza.
Bayanin ya ce dakarun sa kai na Hashd sun cafke wasu kusoshin kungiyar ta Daesh guda hudu a yankin na Nahrain, kuma sun mika su ga jami’an tsaron kasar Iraki.
Kungiyar dakarun sa kai na al’ummar kasar Hashad Sha’abi dai ita ce ta kori ‘yan ta’addan Daesh daga yankunan da suka kwace iko da su a cikin kasar Iraki a shekarun baya, kamar yadda kuma suka dawo da yankunan da suka kwace ga gwamnatin Iraki, daga cikin muhimman wuraren da Hashd daga hannun ‘yan ta’adda har da birnin Mausul, wanda Daesh ta mayar da shi babbar hedikwatar abin da take kira daular musulunci.
/129