23 Maris 2020 - 13:34
Rasha, Cuba Da Sin, Na Taimakon Italiya A Yaki Da Coronavirus

Kasashen Rasha, da Cuba da kuma China, sun sanar da aikewa da taimako zuwa Italiya, domin taimaka mata a yaki da cutar coronavirus dake ci gaba da kisa a kasar.

(ABNA24.com) Italiya dai ita ce kasa inda cutar coronavirus, ta fi yin kisa a duniya.

Kasashen Rasha da Cuba sun aike da tawagogi na likitoci, yayin da ita ma kasar ta China ta sanar da aikewa da kwararun likitoci da kuma kayan asibiti.

Kawo yanzu mutane 4,825 ne cutar ta Covid 19 ta kashe a Italiya, sai kuma wasu 53,578 suka kamu da ita, ciki kuma 6,000 suka warke.

342