23 Maris 2020 - 13:32
Iran : Shugaba Rohani Ya Caccaki Siyasar Amurka

Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya sake caccakar siyasar Amurka kan kasarsa.

(ABNA24.com) Dakta Rohani, ya kara da cewa matsin lamba da takunkumi ba za su taba yin nasara kan Iran ba, kuma ba za su sauya komai ba.

A daya bangaren shugaba Rohani, ya ce halin da ake ciki yanzu a duniya na yaki da cutar coronavirus, ana bukatar hadin kan kasa da kasa domin murkushe cutar.

Amma amfani da takunkumi ko wani abu makamancin haka, musamman toshe kudaden da ake bukata don taimakawa sha’anin kiwaon lafiya zai yi tasiri sosai a yakin da Iran ta ke da annobar.

Ya ce babu wata kasa a doron duniyar nan da ita kadai za ta iya jurewa babbar matsalar da ake ciki a halin yanzu, musamman idan aka haramta ma ta shiga harkokin kudade a duniya da kuma hana ta sayen kayayakin da ta ke bukata.

342