9 Maris 2020 - 10:50
Shugaban Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran Yana Ci Gaba Da Ziyarar Aiki A Kasar Iraki

A jiya Lahadi shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran din, Ali Shamkhani ya gana da firai minista na rikon kwarya, Adil Abdulmahadi, inda su ka tattauna alakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a wannan yankin na gabas ta tsakiya.

(ABNA24.com) A jiya Lahadi shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran din, Ali Shamkhani ya gana da firai minista na rikon kwarya, Adil Abdulmahadi, inda su ka tattauna alakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a wannan yankin na gabas ta tsakiya.

Tun da fari,an yi wata ganawar a tsakanin Ali Shamkhani da kuma manyan jami’an tsaron kasar, da su ka hada mai bayar da shawara akan harkokin tsaron kasa, Falih Fayyadh, da shugaban hukuma leken asiri Mustafa Khazimi, sai kuma shugaban jam’iyyar “Tayyarul-Hikimah” Sayyid Ammar Hakim.

A shekaran jiya Asabar ne dai shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran din ya fara ziyarar aiki a kasar Irakin, bisa gayyatar jami’an gwamnatin kasar.



/129+