(ABNA24.com) Kakakin ma’aikatar tsaron Iran da fasahar sararin samaniya, Sayyid Ahmad Hussain ya fada a jiya Lahadi cewa; Na’uar da Iran ta kera domin harba tauraron dan adam, ta yi nasarar harba tauraron dan adam na Zafar, sai dai ba ta iya cimma hanzarin da ake bukatuwa da shi ba, domin isar da tauraron dan adam din cikin sararin samaniya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; Dukkanin matakan da su ka gabaci harba tauraron dan adam din sun kasance cikin nasara, kama daga kan gwaje-gwajen da aka yi,zuwa zuba makamashin da ake da bukatuwa da shi da kuma dora tauraron dan adam din akansa.
Iran ta gina cibiyar harba tauraron dan adam a gundumar Semina, wacce a baya an harba wasu taurarin na dan adam daga cikinsu da ta harba har sau shida.
/129
10 Faburairu 2020 - 08:29
Lambar labari: 1009213
Na’urar “Simorhg” Ta Yi Nasarar Harba Tauraron Dan “adam Na Zafar Duk Da Matsalar Da Aka Fuskanta