27 Janairu 2020 - 06:51
​Saudiyya Za Ta Yanke Taimakon Da Take Bawa Masallatai A Kasashen Waje

Gwamnatin Saudiyya na da anniyyar yanke taimakon da take bayarwa domin daukar nauyin masallatai a kasashen waje.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran IQNA, ya nakalto jaridar Middl East Mirror tana bada wannan rahoton.

Muhammad Bin Abdulkarim Issa tsohon ministan shari’a na kasar Saudiyya, kuma babban sakataren kungiyar hadin kan duniyar musulmi (Muslim World League) ya bayyana cewa, gwamnatin Saudiyya za ta daina daukar nauyin masallatai a kasashen ketare.

A zantawarsa da jaridar “Le Matin Demanche” ta kasar Switzerland, Muhammad Bin Abdulkarim Isa ya bayyana cewa, a halin yanzu suna shirin mayar da batun kula da masallatan ga hukumomin kasashen da masallatan suke cikinsu. Isa ya ce a yanzun haka sun fara magana da hukumomin Switzerland kan batun babbanmasallacin Geneva don samun wanda zai dauki nauyinsa.

Yace manufar hakan ita ce rage yawan ayyuka da suka shafi kula da masalatai da kasar take, domin kuwa hakan wani abu ne wanda za a iya hadakai da hukumomin kasashe domin aiwatar da shi.



/129