Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA-ta rawaito wani Tsohon wakilin majalisar tarayyar turai yace kisan kassim Sulemani laifin yaki ne yan. ya kara da cewa:manufar 'yan mulkin mallaka itace ganin bayan juyin musulunci ne.ya yin da yake wata tattaunawa da tashar almayadin yace:kissan Kassim Sulemani wani nau'i ne na ta'addanci a bayyane.
Javier COUSO ya kara da cewa: kashe wani babban jami'in sojan Iran a cikin kasar Iraki ya sabawa doka kuma a lokaci guda keta 'yanci wata kasa ne. a gefe guda kuma ya yaba wa kokarin Janar Sulemani wajan yakar yan ta'adda a Syria da ma yankin baki daya, ya kuma yabi hakurin Iran ta hanyar ramuwa da makamai masu lizzami a matsayin gargadi ga masu wuce gona da iri.