ABNA24- ta rawaito Quraishi ba ce wa; Abin da Pakistan ne take son gani a bude tattaunawa a tsakanin Iran da Saudiyya domin warware rashin fahimtar juna da ke tsakaninsu.
Ministan harkokin wajen kasar ta Pakistan ya kuma bayyana yadda kasarsa take da kyakkyawar alaka a tsakaninta da kasashen Iran da Saudiyya, sannan ya kara da cewa; Bude wani sabon rikici a cikin wannan yankin ba abu ne da zai yi kyau ba, kuma muna son ganin zaman lafiya da ci gaba sun sake dawowa a cikin yankin.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai minstan harkokin wajen Saudiyya Faisal Bin Farhan ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta bude tattaunawa da Iran.