23 Janairu 2020 - 18:38
Brian Hook Ya Yi Barazanar Kashe Janar  Qaani

Wakilin Amurka na musamman kan Iran ya maimaita zargin mara tushe akan Kwamandan Qassim Suleimani, kwamandan rundunar Quds, yana mai cewa: "Idan Kwamandan Qa Qaani yana son ci gaba da bin tafarkin Sulemani to shima ya shirya mutuwa.


Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito Bryan Hook, manzon Amurka na musamman kan harkokin Iran ya yi barazanar kashe kwamandan sojojin Quds,

A wata hira da ya yi da kafanin yada labarai na Saudiyya ,wakili Amruka na musamman kan harkokin waje yace palomar Kasim Sulaimani itace makomar sabon kwamandan Quds idan ya ci gaba da bin tafarkin Sulemani din.

wannan jami'in na Amurka ya sake maimaita ikrarin shugaba Trump na cewa sun kashe  Kasim Sulemani ne don Kate kansu.