ABNA24-Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zareef ya ja kunnen kasashen turai dangane da shirinsu na maida batun shirin nukliyar kasar zuwa kwamitin tsaro na MDD, inda ya ce idan sun yi hakan mai yuwa Iran ta fice daga yerjejeniyar NPT kwata-kwata.
Zarif ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya kira a safiyar yau Litinin a nan birnin Tehran. Ministan ya kara da cewa Iran ba ta fara daukar matakan jingine yerjejeniyar nukliyar kasar daka-daki ba, sai bayan ficewar Amurka daga yerjejeniyar a shekara 2018, sannan da cimma yerjejeniyar da kasashen turai uku, Britania, Faransa da kuma Jamus, kan cewa za su biya wusu bukatun Iran don hana yerjejeniyar mutuwa, amma har zuwa lokacin da ta fara jingine yerjejeniyar basu cika ko da daya daga cikin alkawuran da suka dauka ba.
Kafin haka, Zarif ya ce ya aikewa tsohuwar jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na tarayyar Turai ta lokacin, wato Federica Mugareni wasiku har uku don tunatar da su kan alkawarin da suka dauka, da kuma cewa Iran tana da zabi mai yawa idan sun kasa.