15 Janairu 2020 - 18:04
​Zarif: Trump, Pompoe, Daesh Ne Suke Farin Ciki Da Kisan Sulaimani

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Trump da ministan harkokin wajensa gami da ‘yan ta’addan daesh ne kawai suke farin ciki da kisan Kasim Sulaimani.

ABNA24- Presstv ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a yau a gaban taron tsaro na kasa da kasa a birnin New Delhi na kasar India, Zarif ya bayyana kisan Kasim Sulaimani da cewa babban laifi ne Amurka ta tafka.

Ya ce wannan laifi ya shafi bangarori da dama, da hakan ya hada da keta dokokin kasa da kasa, baya ga haka kuma wannan babbar hidima ce ga ‘yan ta’adda, wadanda hakan ke nuni da cewa da wadanda suka kasha Sulamaini da ‘yan ta’adda duk aikinsu guda ne.

Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, a lokacin da wasu suke karyar yaki da ta’addanci, kuma suke taimaka ma ‘yan ta’adda, hakan ya tabbatar da karyar abin da suke rayawa, daya daga cikin misalign hakan shi ne kisan Sulaimani, domin kuwa ya taiamaka wajen kawar da ‘yan ta’adda a kasashen da ‘yan ta’adda suka addabe su, kuma ya yi hakan ne bisa gayyatar gwamnatocin wadannan kasashe, da hakan ya hada har da Iraki.