(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran IQNA, a yau ne aka gudanar da sallar janazar marigayi sarki Qabus na kasar Oman, wanda ya rasu jiya yana dan shekaru 79 a duniya bayan fama da rashin lafiya.
Sarki Qabus ya dare kan mulkin kasar Oman bayan mahaifinsa, inda aka sanya ranar 23 ga watan Yuli ta zama muhimmiyar rana a kasar, saboda aranar ne ya karbi mulkin kasar.
Sarki Qabus ya taka rawa wajen ganin ya mayar da hankali ga ayyukan sulhunta rikice-rikice tsakanin kasashe, musamman na yankin gabas ta tsakiya.
/129
12 Janairu 2020 - 04:29
Lambar labari: 1001463
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da sallar janaza ta sarki Qabus na kasar Oman a yau.