(ABNA24.com) Kafafen watsa labarun kasar Oman sun sanar da rasuwar sarkin kasar Qabus Bin Sa’id bayan da ya yi fama da rashin lafiya
Sarki Qabus ya rasu yana dan shekaru 79 a duniya
Fadar sarkin kasar ta Oman ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku da kuma bayar da hutu a fadin kasar. Har ila yau za a sauko da tutar kasar kasa-kasa har na tsawon kwanaki arba’in.
A karkashin tsarin mulkin kasar ta Oman majalisar masarauta ce ke da hakkin sanar da wanda zai zama sabon sarki a cikin kwanaki uku daga mutuwar sarki.
A kasar ta Oman dai babu yarima mai jiran gado.
Tun a ranar 23 ga watan Janairu na 1970 ne dai Qabus ya zama sarkin Oman, da hakan ya mayar da shi wanda ya fi dacewa akan karagar mulki a gabas ta tsakiya
/129
11 Janairu 2020 - 06:07
Lambar labari: 1001243
Kafafen watsa labarun kasar Oman sun sanar da rasuwar sarkin kasar Qabus Bin Sa’id bayan da ya yi fama da rashin lafiya