8 Janairu 2020 - 05:56
​Muqtada Sadr Ya Aike Wa Trump Da Wasika Ta Hanyar Twitter

Sayyid Muqtada Sadr ya aike da wata wasika mai zafi zuwa ga Trump ta hanyar shafinsa na twitter.

(ABNA24.com) A cikin sakon nasa Muqtada Sadr ya caccaki shugaban kasar Amurka Donald Trump, inda bayyana shi a matsayin mutumin da ba shi da masaniya kan harkokin siyasar duniya, face ayyukan badala, da tambele a gidajen rawa da caca.

Haka nan kuma Muqtada Sadr ya gargadi Donald Trump dangane da barazanar da ya yi ta kakaba kasar Iraki takunkumi, matukar dai gwamnatin kasar ta dage a kan ficewar sojojin Amurka daga kasar.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, makaman da Trump yake takama da su kuma yake yin barazana da su a kan al’ummomin duniya, ba za su amfanar da shi da komai ba.

Inda ya tambayi Trump cewa; shin ka manta kashin da Amurka ta sha ne a yakin da ta kaddamar kan al'ummar kasar Vietnam ne?

Muqtada Sadr ya kara da cewa, abin mamaki ne yadda mutumin da a jiya yake da’awar cewa ya shiga Iraki ne domin ‘yantar da ita daga ‘yan ta’adda, a yau kuma shi ne yake yi mata barazana da ta’addanci.

Sadr ya ce; idan ka ji nasiha ka tsira, idan kuma ka ci gaba da yin kememe da tsaurin kai to za ka gamu da gamoka, mu ba masu neman yaki ba ne, amma za mu yaki idan aka yake, wanda ya fara yaki shi ne mafi zalunci.

Daga karshe Muqtada Sadr ya jaddada cewa al’ummar Iraki ba za su taba mika wuya ga bakaken manufin Amurka ba, domin kuwa sun zabi su rayu ne a cikin ‘yanci da daukaka, ba a cikin kaskanci na bauta ba.


/129