16 Yuli 2026 - 17:10
Source: ABNA24
Iran: Ta Kai Hari A Kan Cibiyar Umarni Da Sarrafawa Ta Amurka A Jordan

Rundunar sararin samaniya ta dakarun juyin musulunci ta kai hari a kan sansanin Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na "Khaibar Shikan," kuma ta yi kira ga al'ummar Jordan da su kai hari ga muradun Amurka yar mamaya su tsarkake ƙasarsu daga gare su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Dakarun Juyin Musulunci na Iran, a yau Alhamis, sun sanar da cewa mayakan rundunar sararin samaniyarsu sun sami nasarar lalata rumfunan ajiye jiragen yaƙi na Amurka, baya ga sabuwar cibiyar umarni da sarrafawa ta Amurka a yankin yammacin Asiya.

Dakarun Juyin Musulunci, a cikin wata sanarwa ta soji, sun bayyana cewa wannan hari na musamman ya kai ga wani babban sansanin sojojin mamaya na Amurka a yankin Al-Azraq na Jordan, suna nuni da cewa an aiwatar da aikin cikin nasara ta amfani da makamai masu linzami na ballastic na "Khaibar Shikan" na zamani.

A cikin wata magana kai tsaye ga al'ummar Jordan, dakarun juyin musulunci sun aika da sako ga al'ummar Jordan inda suka ce: "Ya ku al'ummar Jordan masu kishi, kun fi kowa sanin laifukan Amurka da yahudawa a nan kusa fiye da kowace al'umma."

Dakarun Juyin Musulunci a cikin sanarwarsu sun buƙaci al'ummar Jordan su hana amfani da ƙasarsu wajen ta'addanci, sun kara da cewa: "Kada ku ƙyale a yi amfani da ƙasar Jordan mai tsarki, wadda take kasar annabawa, don aikata waɗannan laifuka a kan yara."

Dakarun Juyin Musulunci na Iran sun ƙarasa kiran su da cewa: "Ku kai hari ga muradun Amurka da dukkan ƙarfin da kuka ke da, kuma ku tsarkake ƙasarku daga ƙazantar mamaya na Amurka."

A nasu bangaren, dakarun juyin musulunci na Iran, a jiya, sun sanar da kai hari a kan sansanonin Amurka a Kuwait. Haka kuma, dakarun juyin musulunci sun yi magana da al'ummar Kuwait, suna tabbatar da cewa Tehran ba ta da wata ƙiyayya gare su, a'a, tana son su saboda darajarsu da kyawawan halayensu.

Dakarun Juyin Musulunci sun yi nuni da cewa aikin ba komai bane face martani ga laifukan Amurka, domin fiye da watanni 4 da suka gabata sojojin Amurka suka fara yaƙi bayan kai hari ga jagora na duniya Sayyid Ali Khamene'i.

Saboda haka, dakarun juyin musulunci sun yi nuni da cewa "tushen yawancin ta'addanci a wannan yaƙi su ne sansanonin sojojin Amurka da ke ƙasar Kuwait mai tsarki."

Dakarun Juyin Musulunci sun yi tsammanin cewa al'ummar Kuwait ba za su rasa wata dama ba don "lalata cibiyoyin Amurka masu ta'addanci da kuma 'yantar da ƙasashen Musulunci daga sansanonin mamaya."

A cikin sa'o'in dare da sanyin safiya na Laraba zuwa Alhamis, Amurka ta kai hare-hare da dama da suka shafi tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas, da garuruwan Rask da Kanarak a lardin Sistan da Baluchistan, da wurare a birnin Ahvaz, da kewayen tsibirin Qeshm.

Ta'addancin Amurka yana ci gaba da hare-harensa a kan yankuna a kudancin Iran tun 'yan kwanakin da suka gabata, yayin da Iran ke mayar da martani ta hanyar kai hari a kan sansanoni da cibiyoyi da wuraren Amurka masu muhimmanci a yankin.

…….

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha