Kamfanin dillancin
labaran ƙasa da ƙasa na AhlulBaiti (As) -ABNA- ya ruwaito maku cewa: an gudanar da bukukuwan maulidin manzon
Allah Annabi Isa (As) da yammacin yau litinin tare da halartar Ayatullah Raza
Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya da Robert
Lugal, Archbishop na Toulouse na kasar Faransa da Hujjatul Islam Walmuslimin
Saeed Jazzari shugaban jami'ar kasa da kasa ta Ahlulbaiti (AS) da dalibai na
kasashen duniya da baki daga kasashe daban-daban an gudanar da shi a jami'ar
Ahlulbaiti (AS).
A cikin wannan biki Ayatullah Reza Ramezani Gilani ya bayyana cewa: Annabin Musulunci (SAW) da Annabi Isa Almasihu (A.S) Manzanni ne da suka kawo soyayya, tsira da adalcin sama, kuma masu nusatarwa ga batattu don su koma zuwa ga bautawa Allah cikin sani.
Ya kara da cewa: A bisa akidar musulmi, addinan Ubangiji kamar jiki guda daya ne, dukkansu sun samo asali ne daga gaskiya guda daya ta Ubangiji, Annabawan Ubangiji su ne mafi kamala kuma fiyayyen halittun talikai, kuma zababbun Allah madaukakin sarki don nusatarwa da kuma ya shiryar da mutane".
Babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kira Annabawa a matsayin abin koyi na daidaiku da zamantakewa na bil'adama inda ya bayyana cewa: Musulmai suna daukar Annabi Isa (AS) a matsayin daya daga cikin manyan annabawan Allah guda biyar, shi manzon Allah da ke kira zuwa rahama, albarka da shiriya ga mutane da haske mai shiryarwa a cikin duhun shirka, zalunci da gurbacewar duniya da zunubi da bata wadda ta kai dukkan mutane zuwa ga tafarkin Allah.
Ya ambaci gaskiya da rikon amana da kyautatawa da neman alkhairi da yaki da zalunci da fasadi a matsayin fitattun halaye na annabawa: misali, rikon amana ga wahayi da sadar da sakon Allah, da jefa jikinsu ga wahala da matsi don neman yardar Allah, da yin hijira a tafarkin Allah yana daga cikin sifofin Manzon Allah (SAW), kamar yadda ya zo a cikin addu’ar littafin Sajjadiyah, dalilin hijirar Annabi da zamansa shi ne yardar Allah da zartar da umurnin Allah.
Ayatullah Ramezani Gilani ya kara da cewa: Imam Sajjad (a.s.) yana ganin alkawarin Allah Madaukakin Sarki dangane da ceton Manzon Allah (s.a.w) a matsayin tabbatacce, yana mai cewa alherin cetonsa da karbar cetonsa ga iyalan gidansa tsarkaka da kuma al'ummarsa muminai ya fi fiye da abin da kuka yi masa alkawari.
A wani sashe na jawabinsa, ya bayyana shaksiyar Annabi Isa As a cikin littafin "Confessions" na St. Augustine kuma ya jaddada cewa: A cikin wannan littafi, an bayyana shaksiya da halaye kamar jagoran zaman lafiya, mai ceton rayuwar ɗan adam da kuma mai kama hannun 'yan adam a wani gida, ana kashe shi domin Kaffarar zunuban mutane da sadaukarwa ta hanyar cetonsa duka wadannan halaye da sifofin an fade su ne ga Annabi Isa (AS).
Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (A.S) ya ci gaba da cewa: Dangane da sadukarwar Annabi Isa (A.S) Saint Augustine ya ce da ba don haka ba, da mutum zai ci gaba da zama a cikin kuncin zunubai kuma ya sake dawwama. Kuma ya kara ikrari da cewa idan da bai yi tawassuli da Masihu ba, da ba zai kai ga Allah ba, zai fuskanci mutuwa da tabewa ne kawai.
Shekh Ramazani Gilani ya yi nuni da cewa, bisa ga akidar Augustine, dabi’ar Annabi Isa (AS) mutum ne “tsarkake” na Allah kuma cikakken mai ibada, ya ce: Annabi Isa (a.s) ya yarda da ya mutu domin ya ceci ‘ya’yan Adam, ana daukarsa a matsayin dan tsakani a wurin Allah.
Ya ce: A cikin abinda Augustine yayi Imani da shi akwai cewa, ana daukar Annabi (AS) matsakanci na kwararar alherin Allah, ba wai akwai manzon wahayi ba, sai dai ana daukarsa a matsayin siffar wahayin Allah. Kamar yadda a cikin addinin Musulunci wahayin Ubangiji da Alkur’ani suka sauka a zuciyar Manzon Allah (SAW), a mahangar Kiristanci, wahayin Ubangiji shi ne Masihu da kansa (A.S).
Ramezani Gilani ya jaddada cewa a lokacin zamansa a tsakanin mutane, Yesu bai yi kasa a gwiwa ba na dan lokaci wajen yaki da zalunci da kira zuwa ga alheri kuma yana daya daga cikin wadanda suka fi fama da yaki da zalunci da fasadi, ya kuma ce: Wannan darasi ne da ya kamata kiristoci ya kamata su yi koyi. Kuma musulmi su sani, idan suka zamo yan kallo ga ayyukan azzalumai da makiya bil'adama suka bar fili ba kowa, to Azzalumai ba za su bar wata alama ta wuraren ibada da cibiyoyin bautar Ubangiji ba.
Babban magatakardar Majalisar Ahlul Baiti (AS) a karshe yayi ishara da cewa: Tafarkin Manzon Allah (SAW) da Isa Almasihu (AS) ita ce isa ga adalci da mutuntaka da soyayya, su ne ma’auni na adalcin sama, kuma masu nusatarwa ga batattu da masu rudu zuwa ga bautawa Allah kuma su ne masu dauke da sakon tsira da kubutar yan Adam…