Tashar Isra'ila ta 12 ta bada rahoton cewa Amurka ce ta kai harin a Sana'a a daren yau.
Kafar tashar AlHadath ma ta ruwaito cewa Amurka ta sake kai wa filin jirgin saman Sana'a hari a wanda a kwanakin baya ma ta kai masa hari.
Tashar talabijin ta Isra'ila ta Channel 12 ta yi ikirarin cewa: Isra'ila za ta ci gaba da kai hare-hare kan kasar Yemen cikin makonni masu zuwa
Ita Majiyar Yaman ta rawaito cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa biyo bayan harin da jiragen yakin kasar Amurka suka kai a Sana'a babban birnin kasar.
Majiyoyin yahudawan sahyoniya sun sanar da cewa, harin na baya-bayan nan da aka kai a birnin San'a an kai shi ne ba tare da kasancewar sojojin Isra'ila ba.
Mayakan Amurka da Birtaniya sun yi ruwan bama-bamai ne a wurare da dama a Sana'a, babban birnin kasar Yemen.
Suma Majiyoyin Larabawa sun bayyana cewa, filin jirgin saman Sana'a ne aka kai hare-haren a wannan dare.