Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya kawo maku rahotan cewa: Sayyid
Abdul Malik Al-Huthi aciin bayaninsa yau ya anbaci cewa: Laifukan yaki da kisan
kiyashi ga al'ummar Palastinu gwaji ne ga lamiri da kimar al'ummar dan Adam.
Shiru kan kisan kiyashin da ake yi a Gaza na nufin al'ummomin bil'adama sun yi
watsi da mutuncin dan Adam da 'yancin rayuwa.
Abin da makiya yahudawan sahyoniya suke yi ya ginu ne a kan mahanga ta karya kuma cin mutunci ne ga al'ummomin bil'adama. Yunkurin dalibai da zanga-zangar da aka yi a sassa daban-daban na duniya na yin Allah wadai da abin da ke faruwa a Gaza ya yi matukar tasiri wajen wayar da kan jama'a tare da fallasa karyar yahudawan sahyoniya a tsakanin al'ummar duniya musamman Amurka da Turai.
Daya daga cikin munanan laifukan da makiya suka aikata shi ne kisan wasu dattijai 3 ‘yan gida daya, daya daga cikinsu ya yi shahada a lokacin azabtarwa, biyu kuma an kashe su ta hanyar murkushe su da tankokin yaki. Laifin kisan gillar da aka yi a Gaza ya kamata ya farkar da lamirai ɗan adam kuma ya farkar da da wani yanayin jin nauyi da ya hau kansa a cikin lamirinsa.