Tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, Imam ya jaddada gudanar da zaben raba gardama. Don haka ne aka gudanar da kuri'ar raba gardama a ranar 12 Faruddin 1358 kuma kashi 98/2 na masu kada kuri'a ne suka kada kuri'ar kafa Jamhuriyar Musulunci. Bayan haka, an gudanar da zabuka daban-daban na tsara kundin tsarin mulki da amincewa da zaben wakilan majalisar Musulunci. Imam a kowace rana a gidansa da kuma Madrasa Faizia da ke birnin Qum, domin tabbatar da shika-shikan tsarin Musulunci da kuma bayyana kananan manufofi da manyan manufofin gwamnatin Musulunci, ya gabatar da jawabai inda yake ganawa da dubban mabiyansa. Kamar yadda tarihin Imam Khumaini ya nuna ya zo birnin Qum daga Tehran bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a ranar 10 ga watan Isfand shekara ta 1357 kuma yana cikin wannan birnin har ya yi fama da ciwon zuciya (2 ga Bahman 1358). Imam bayan shafe kwanaki 39 yana jinya a asibitin zuciya na Tehran, na wani dan lokaci ya zauna wani a gida da ke yankin Darband a Tehran sannan ya koma wani gida madaidaici na Hujjtul-Islam Sayyid Mahdi Imam Jamarani a unguwar Jamaran ya zauna a wannan gidan har wafatinsa. Kuma Imam Khumaini ya yi wafati ne da misalin karfe 22:20 a lokacin Iran a ranar 13 ga watan Khurdad shekarar 1368.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a farkon shekarun juyin juya halin Musulunci shine kame tarkon masu leken asiri. A watan Aban a shekara ta 1358, labarin ganawar - da ba’a bayyana ba – ta Malam Bazargan da Brzezinski mai ba da shawara kan harkokin tsaro na fadar White House a Aljeriya ya isa Iran. A ranar 13 ga watan Aban ne wasu gungun dalibai musulmi da ke bin tafarkin Imam suka mamaye ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tehran domin samo takardun leken asirin Amurka a Iran. Kwana daya bayan faruwar wannan lamari, gwamnatin wucin gadi ta Mista Bazargan ta fadi ta hanyar amincewa da murabus daga Imam Khumaini. Don ƙarin bayani kan dalilan wannan gaggawar murabus, karanta cikakken labarin tarihin Imam Khumaini. Haka nan Imam Khumaini ya goyi bayan yunkurin daliban da kuma kiransa juyin juya hali mafi girma fiye da juyin juya halin farko.
Bayan gwamnatin Bazargan, Abulhassan Bani Sadr ya lashe zaben shugaban kasa. Tun farko dai Bani Sadr ya ginu ne bisa rashin jituwa da tafarkin Imam da adawa da malaman addini. A lokacin yakin Iran da Iraki, wakilan da ke da alaka da Bani Sadr, wadanda suke ganin wanzuwar kansu a matsayin masu haifar da matsala ga tsarin Musulunci, sun hana a samar da kayan aiki na jama'a da kuma dakarun kare juyin juya halin Musulunci. Rikicin Banisadr ya yi wa hadin kan kasa barazana. Don haka ne Imam Khumaini ya tsige Banisadr daga shugabancin rundunar sojojin kasar a ranar 20 Khordad 1360, bayan da majalisar Musulunci ta kada kuri'ar rashin iya aikinsa.
Bayan faruwar wannan lamari ne mambobi da magoya bayan kungiyar Mujahidin ta Khalq suka fara tashe tashen hankula da suka hada da kisan Shahida Muhammad Ali Raja'i da Shahid Bahunar da yunkurin kashe Ayatullah Khamenei. A duk tsawon wannan lokaci Imam ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da kasar ta hanyar fadakar da al'ummar juyin juya hali da daukar matakai masu tsauri da gaggawa. Daya daga cikin muhimman nasarorin da Imam Khumaini ya samu a cikin wadannan shekaru bayan juyin juya halin Musulunci, shi ne kara wayar da kan al'umma da kuma fahimtar da al'umma tare da samar da wani nauyi da kuma karfin nazari a cikin lamurran siyasar wannan zamani. Wannan batu ya kasance har mutane suka rika rera wakar bayan shahadar Raja'i da Bihishti cewa: "Amurka tana cikin wane tunani ne alhali Iran cike take da Bihishtiyawa"?.
Imam Khumaini A Zamanin Yakin Kariyar Kai Mai Tsarki
Imam Khumaini a lokacin yakin shekaru takwas da aka yi tsakanin Iran da Iraki, bisa akidarsa ga Jihadi a matsayin wajibcin Ubangiji, tun daga farko ya ba da umarnin gwagwarmaya a gaban makiya masu mamaya.Ya shiryawa mutane wasu gungu na jawabai da kuma fitar da sakwanni akai-akai yana ami zaburar da su shirya akan yaki mai tsawon zango.
A kwanakin farko na yakin, dubun dubatan mutane da masu aikin sa kai ne suka fita fagen daga domin taimakawa dakarun soji, kuma a matakin farko sojojin Musulunci sun dakile ci gaban makiya.
A lokacin yakin kariyar kai mai tsarki, shima gwagwarmaya a gaban sojojin Iraki ta ci gaba bisa nusarwa da shiriyarwa da umurnin Imam Khumaini, kuma abin da aka cimma wata babbar nasara ce; Domin kuwa a karon farko cikin shekaru dari biyu da suka gabata, Iran ba ta yi asarar ko da wani bangare na kasarta ba a yakin da bana tamka da tamka ba, kuma ba ta nemi taimako daga mashawartan kasashen waje ba, ta tsaya da kafafunta namijin tsayuwa, ta kai ga dogaro da kai a masana'antun tsaro, ko a lokacin da yaki ya yi zafi, ba tai sakaci wajen zuwa rumfunan zabe don tantance makomarta ba, ta kuma tabbatar da kanta a matsayin mai karfin da zata iya tallafawa wadanda ake zalunta a duniya.
Amincin Allah Ya Ya Kara Tabbata Gareka Ya Ruhullah Muna Sallama Gareka Tun Ranar Da Aka Haifeka Da Har Zuwa Ranar Da Ka Koma Zuwa Ga Mahaliccinka Har Zuwa Ranar Dawwamar Jamhuriyyar Musulunci Da Ka Jagoranta