Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

5 Faburairu 2024

12:50:59
1435403

Halartar Mutane Dayawa A Zaɓe Shi Zai Tabbatar Da Ikon Ƙasa Da Tsaro.

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Dinbin Halartar Mutane A Tattakin 22 Bahman Alama Ce Ta Karfin Ƙasa

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma kara da cewa idan aka gudanar da zabuka masu kayatarwa, za a iya ganin karfin kasa da tsaron kasa ya tabbatar da cewa: Tare da halartar mutane a fagen da lura da karfin tsarin kasa za a kawar da barazanar makiya, saboda ikon kasa da karfi, Yana haifar da tsaron kasa.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta cewa: Jagoran juyin juya halin Musuluncin a wata ganawa da yayi a yau da kwamandoji da ma'aikatan sojojin sama da na sojojin kasar ya kira mubaya'ar da akayiwa Imam Khumaini a ranar 19 ga Bahman 1357 a matsayin "Mai hanzartarwa" na juyin juya halin Musulunci, bayanin irin rawar da kebantattu wadanda sukai hanzari wajen mubaya’ar ke takawa - a ma'anar kungiyoyi da jigogin da ke aiki tare da daidaito da jaruntaka da sanin lokacin ganewa da dacewar asali – sun yi aiki a lokacin da ya dace. Ya kara da cewa: Kebantattun ta hanyar aiwatar da hanzarin da ya dace sun dauki nauyi mai nauyi wajen samar abunda ake bukata don tabbatar da manufofin juyin juya halin Musulunci.

Har ila yau Ayatullah Khamenei ya dauki cewa duk yadda halartar al'umma yayi yawa a zaben ranar 11 ga watan Isfand a matsayin tabbacin tabbatar da ikon kasa da tsaron kasa sannan kuma ya jaddada cewa: cikin yardar Allah al'ummar kasar za su halarci tattaki na kasa da kasa na ranar 22 ga watan Bahman. sannan kuma ta hanyar kare juyin juya hali za su nuna biyayyarsu ga Imam Khumaini

Babban kwamandan rundunar ya dauki wannan lamari mai ban mamaki na mubaya’ar da wasu gungun abokan tafiya da sojojin sama suka yi wa Imam Khumaini a ranar 19 ga watan Bahman shekaru 46 da suka gabata a matsayin darasi maras iyaka, ya kuma kara da cewa: Sojojin sama, tare da sadaukar da kai da wannan aiki na gaskiya da jajircewa wajen shigansu gaba-gaba cikin juyin juya hali sun ciri tuta. A cikin kwanakin suka biyo baya ta hanyar tinkarar harin da dakarun tsaron Shah suka kai a cibiyar sojojin sama da ke Tehran, ya sanya jama'a da matasa sun fito kan tituna cikin shaukin da sha'awa. Wanda ya zamo ta dalilin hakan cikin nasarar juyin juya halin Musulunci a ranar 22 ga Bahman sun taka muhimmiyar rawa ta "masu hanzarin na kawo dauki a Lokacin da ya dace".

Haka nan kuma yayin da yake ishara da samar jihadi na dogaro da kai a cikin sojojin sama 'yan watanni kadan bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Irin wannan ruhin karfi da jajircewa da karfin ruhi ne ya sanya sojojin sama suka zama majagaba da kuma kara kaimi a cikin juyin juya halin Musulunci wajen samar da jihadi na dogaro da kai.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya lisafta sojojin sama na zamanin Tagut da cewa gaba daya suna hannun kuma karkashin ikon Amurkawa ta fuskar umarni da manufofi da kayan aiki, sannan ya kara da cewa: Masu imani da juyin juya hali tare da jihadi mai dogaro da kai sun canja sojojin sama daga mallakin Amurka kuma gaba daya suka zamo dakarun Iran, inda suka nuna jagorancinsu da ikon kawo sauyi.

Ya kira mallakar ginshikai masu hanzari da tsara abubuwa a matsayin ci gaba da bukatuwa na juyin juya hali da kuma yunkuri na al'umma masu girma da manufa sannan ya ce: Bisa la'akari da kwarewar tarihi, a sannu ahankali manya-manyan yunkurori suna yin rauni har ma suna komawa baya, wanda samuwar wadannan masu hanzarin yana hana wannan annoba aukuwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira wasu daga cikin abubuwan masu jan hankali na cikin gida na juyin juya halin Musulunci da suka hada da yaki da zalunci da azzalumai, tsayin daka wajen tunkarar masu cin zarafi na duniya, mai da hankali ga al'ummar duniya da makomar kasar, a lokaci guda kuma suna mai da hankali sosai kan ruhi da tarukan addini, a matsayin sababin ci gaban sabon girma da kuma maye gurbin wurare wadanda suka mutu, inda yace: Duk da wadannan abubuwan jan hankali, juyin juya halin Musulunci da kasa na bukatar masu hanzari don kada mu yi kasala da rauni a manyan ayyuka.

Ayatullah Khamenei ya dauki waɗannan keɓantattun Ginshikai a matsayin masu kara kaimi na hakika, ya kuma ce a cikin wani muhimmin batu: Ma'anar Keɓantattu ba suna ne kawai ba; A maimakon haka, su ne mutane ginshikoki masu yin aiki da tunani da ilimi da fahimta a cikin kowane nau'i na al'umma kuma suke gudanar da ayyukansu cikin karfi da jajircewa a kan lokaci ba tare da bin yanayi ba.

Ya kara da cewa: Duk wanda yake cikin masana ilimi, dalibai, 'yan siyasa, malamai, 'yan kasuwa, 'yan jarida, sojoji da duk wani nau’ikan mutane da ya yi aiki da fahimtar al'amura wajen fahimtar bangaren abokai da abokan gaba ana daukarsa daya daga cikin kebantattu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira aiki da irin rawar da kebantattu suke da shi a cikin lamurra masu tsanani yana mai cewa: kamata ya yi Kebantattu su kiyaye gaba daya alkiblar yunkurin al'umma, kuma kada su bari wannan yunkuri ya karkace, idan aka yi watsi da wannan aiki, to kuwa za a fuskanci matsaloli wanda zai kawo matsaloli na tarihi.

Ya dauki shakku da jinkiri ko cin amana da hada baki da wasu kebantattu da aka yi a yakin Safin a matsayin misali na gafala mai cutarwa a tarihin Musulunci, ya kuma yi nuni da cewa: A cikin tarihin Musulunci, akwai lokuta da dama wadanda kebantattu da masu hankali suka yi kokwanto a lokacin da ake bukata saboda shakku, tunani, kasala da kuma a wasu lokuta cin amana, ba su halarta a kan lokaci ba kuma wannan rashin kulawa da ayyukansu da su ka yi yayi mummunan tasiri ga wasu  jama’ar mabiya.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa bangaren makiya yana da wani shiri na musamman ga Kebantattun mutane ya kuma kara da cewa: Manufar makiya ita ce Kebantattun mutane ta hanyar shagaltuwa da neman sababi da janyo su zuwa morewa da jindadin duniya, A cikin yanayi da gurare masu mahimmanci, ya zamo basu iya aikata aikin daya dace da taka rawarsu ta masu hanzari ba.

Ya dauki aikin Khawas a matsayin jihadi don bayyanawa da kawar da shubuhohi da shubuhohi da masu nufin mummunan abu su ke, ya ce: A cikin Alkur’ani mai girma an bayyana misali na takarawar wani mutum mumini, dangane da shirin kasha annabawan Allah guda uku wanda ya jajirce da ƙarfin zuciya da gaskiya wajen kiran mutanen da su bi Annabawan cikin karfaffiyar murya ya bayyana Imaninsa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la'akari da cewa ya zama wajibi masu fada a ji su bayyana hakikanin gaskiyar lamarin da kuma nisantar yin magana biyu da bayyana shakku, sannan ya kara da cewa: A yau, batun Gaza wani fage ne mai tsanani ga kebantattun duniyar musulumci da suka hada da manyan malamai da 'yan siyasa, da manema labarai wajen nuna taka rawarsu..

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin masifun bil'adama da suke faruwa a Gaza tare da goyon bayan da Amurka ke ba wa gwamnatin sahyoniyawan, ya kira bayyana wannan gaskiyar da nufin samar da bukatar gaba dayan al'ummar musulmi daga gwamnatocinsu na kai ga gaci ga gwamnatin sahyoniyawan da cewa aikin kebantattu ne, inda ya ce: kaiwa gaci ba ya na nufin yin yaki da gwamnatin sahyoniyawa ba, amma yana nufin karya dangantakar tattalin arziki da gwamnatin sahyoniyawan.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa al'ummomi suna da karfin ruguza gwamnatoci da tilasta musu katse goyon bayan da suke baiwa gwamnatin sahyoniya yana mai cewa: Duk da cewa wannan mulki mai azzalumi da mai siffar kura ya janyo asarar rayukan mata da kananan yara da marasa lafiya. sannan ta kashe mutane dubu ashirin da ‘yan kai, amma har yanzu wasu kasashen musulmi suna ba ta taimakon tattalin arziki, har ma an ji cewa wasu daga cikinsu suna baiwa gwamnatin sahyoniya makamai.

Dangane da muhimman batutuwan cikin gida, ya dauki zaben watan Maris a matsayin filin da kebantattun za su iya taka rawa acikinsa.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma kara da cewa idan aka gudanar da zabuka masu kayatarwa, za a iya ganin karfin kasa da tsaron kasa inda ya tabbatar da cewa: Tare da halartar mutane a fage da lura da karfin tsarin kasa za a kawar da barazanar makiya, saboda iko da karfin kasa yana haifar da tsaron kasa.

Ayatullah Khamenei ya yi ishara da cewa ranar 22 ga watan Bahman, wato ranar tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci ta gabato, yana mai cewa: Kamar yadda a cikin shekaru 45 da suka gabata, mutane sun fito kan tituna a dukkan garuruwa da kauyuka ba tare da ko da ko da kin fitowa na rana  daya ba, da kansu suna ta rera takensu kare juyin juya halin Musulunci da yin biyayya kuma sun bayyana mubaya'arsu ga Imam mai girma, a bana kuma in Allah ya yarda, jama'a masu daraja za su halarci tattakin na ranar 22 ga Bahman, wanda ke nuni da ikon kasa.

A farkon wannan taro, Amir Birgediya Janar Hamid Wahedi, kwamandan rundunar sojin sama, yayin da yake ishara da jajircewar rundunar sojin sama kan tafarki da kuma makarantar shahidai irin su Babaei da Sattari, ya bayar da rahoto kan shirye-shirye da nasarorin da wannan runduna ta samu a wannan fanni na shekarar da ta wuce.

A daidai lokacin da kwanaki goma na Alfijrin hasken musulunci da kuma jajibirin cikar mubaya'ar tarihi mai cike da tarihi da gungun musulmi suka yi wa Imam Khumaini (RA) a ranar 19 Bahman 1357, gungun kwamandoji da ma'aikatan sojojin sama da Sojojin sun gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci a safiyar yau (Litinin).

an watsa wannan taro kai tsaye zuwa sassan rundunar sojin sama a fadin kasar.