Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

9 Satumba 2023

04:30:14
1392232

Wata Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Afku A Kasar Maroko

A safiyar Asabar ne majiyoyin labarai suka bayar da rahoton afkuwar girgizar kasa mai karfin maki 6.8 a Maroko.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Cibiyar nazarin girgizar kasa ta Turai da Mediterranean ta sanar da cewa, girgizar kasa mai karfin maki 6.9 a ma'aunin Richter ta afku a yankin "Okaimden" da ke tsakiyar Maghreb da karfe 23:11 agogon kasar.

A cewar wannan rahoto, wannan girgizar kasa ta afku a zurfin kilomita 10 a yankin Okaimden.

Har yanzu ba a bayar da cikakken bayani kan barnar da wannan girgizar kasar ta yi ba.