Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

21 Agusta 2023

16:26:10
1388372

Amurka: Ta Umarci Jama'arta Da Su Bar Belarus

A daidai lokacin da yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine yayi tsamari, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bakin ofishin jakadancinta a Belarus ta shawarci 'yan kasar da su gaggauta ficewa daga yankin na Belarus.


 Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto wannan labarin daga Kamfanin dillancin labaran iqna Inada ya habarto bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iran Watch cewa, ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Minsk, babban birnin kasar Belarus, ya sanar a cikin wata sanarwa cewa: Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta umarci 'yan kasarta da su bar Belarus nan da nan."

Sanarwar ta ce ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta shawarci 'yan kasar da kada su yi tafiya zuwa kasar Belarus, sannan ta bukaci 'yan kasarta da ke Belarus da su fice daga kasar cikin gaggawa.

A baya dai gwamnatin Amurka ta gargadi mahukuntan birnin Minsk game da amfani da kasar Belarus wajen kai wa Ukraine hari tare da sanar da cewa sama da sojojin Amurka 8,000 ne ke shirin daukar mataki idan kungiyar tsaro ta NATO ta yanke shawarar fara tura dakarun daukar matakin gaggawa.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar a ranar Alhamis cewa ya umarci sojojin kasar da su fara wani samame na musamman a yankin Donbas. Putin ya ce an bayar da wannan umarni ne bayan da shugabannin yankin da ke gabashin Ukraine suka nemi taimakon sojin Rasha a matsayin martani ga karuwar hare-haren ta'addancin Ukraine.

Dangane da ba da izinin gudanar da ayyukan soji na musamman a yankin Donbas, Vladimir Putin ya ce: Duk kokarin da Rasha ta yi na cimma yarjejeniya dangane da rashin ci gaban NATO a yankin Rasha ya ci tura.

Kasashen yammacin duniya daban-daban da suka hada da Amurka da Ingila da kuma mambobin kungiyar Tarayyar Turai sun kakabawa Moscow takunkumi mai tsanani bayan fara farmakin sojin Rasha a Ukraine. Watanni biyu da suka gabata, gwamnatin Rasha ta mika shirinta na tabbatar da amincin tsaro ga Amurka da kungiyar tsaro ta NATO, wanda ya hada da rashin kasancewar Ukraine a cikin kungiyar tsaro ta NATO da kuma janye sojojin kawancen daga gabashin Turai.