Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

21 Mayu 2023

08:05:05
1367453

Iran Ta Mayar Da Maratani Kan Wasu Batutuwa Da Aka Tattuna A Taron Kasashen Larabawa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, dangane da zargin da ake yi na karya a wasu kudurori da taron shugabannin kasashen Larabawa 32 suka fitar, yayin da yake nuna matukar takaici akan ikirarin da aka ambata a matsayin wani yunkuri ne na gazawar da kungiyar da ta yi a baya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi martani kan ikirarin karya a wasu kudurorin taron kasashen Larabawa daya gudana

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, dangane da zargin da ake yi na karya a wasu kudurori da taron shugabannin kasashen Larabawa 32 suka fitar, yayin da yake nuna matukar takaici akan ikirarin da aka ambata a matsayin wani yunkuri ne na gazawar da kungiyar da ta yi a baya.

Nasir Kanani ya kara da cewa: Ana sa ran kungiyar hadin kan kasashen Larabawa za ta dauki mataki mai kyau kuma mai inganci wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da karfafa hadin kan yankin ta hanyar kauce wa wasu da'awar da ke ci karo da juna a cikin kudurorinta.

A sa'i daya kuma, Kanani ya yi marhabin da kyakkyawar hanyar da wasu kasashen yankin suka dauka na kara yin hadin gwiwa tare da ba da fifiko ga tattaunawa da fahimtar juna.