Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

6 Agusta 2021

22:42:35
1167122

Ra’isi: Wajibi Ne A Cire Wa Iran Takunkumi, Iran Ba Za Ta Yi Watsi Da Haƙƙinta Na Ci Gaba Ba

Sabon shugaban ƙasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewar siyasar matsin lamba da barazana ba za su sanya al’ummar ta yi watsi da haƙƙoƙinta ciki kuwa har da haƙƙinta na ci gaba ba, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da goyon bayan duk wani shiri na diplomasiyya da zai kai ga cire wa Iran dukkanin takunkumin zalunci da aka sanya mata.

ABNA24 : Shugaba Ra’isi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar jim kaɗan bayan rantsuwar kama aiki da yayi da a matsayin sabon shugaban ƙasar Iran a majalisar shawarar Musulunci ta ƙasar inda yayin da ya ke magana kan batun matsin lambar da Amurka da ƙawayenta suke yi wa Iran ya bayyana cewar siyasar matsin lamba dai ba za ta sanya al’ummar Iran su yi watsi da haƙƙoƙinsu ba ciki kuwa har da haƙƙi na cigaban ƙasar ciki kuwa har da fasanarta na nukiliya.

Shugaban ya ce zai goyi bayan duk wani aiki diplomasiyya da zai sanya a cire wa ƙasar takunkumin da aka sanya mata wanda ya ce wajibi ne a cire mata su sai dai kuma ya ce gwamnatinsa ba za ta taɓa amincewa da siyasar amfani da ƙarfi da mulkin mallaka ba.

Yayin da ya ke magana kan ƙarfin da Iran take da shi kuwa, shugaban ya ce ƙarfin da Iran take da shi dai ba zai zamanto barazana ga kowa ciki kuwa har da makwabtan ƙasar ba, face ma dai wani lamari ne da zai ƙara tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin, yana mai sake jaddada aniyarsa da kuma gwamnatinsa na miƙa hannayensu ga maƙwabta da sauran gwamnatoci wajen aiki tare da kuma ƙarfafa alaƙa ta girmama juna.

Yayin da yake magana kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran kuwa, Shugaba Ra’isi ya sake jaddada cewar shirin nukiliyan Iran na zaman lafiya ne don haka Iran ba ta da wani shiri na mallakan makaman nukiliya don kuwa bisa fatawar jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, mallakar makaman nukiliyan ma haramun ne.

Har ila yau kuma sabon shugaban na Iran ya sake jaddada aniyar gwamantinsa na ci gaba da nuna goyon baya ga raunana duniya da kuma dukkanin waɗanda ake zalunta da kuma ƙin amincewa da mulkin mallaka da kuma girman kan ma’abota girman duniya.

Yayin da ya ke magana kan siyasar gwamnatinta ta cikin gida kuwa, shugaban na Iran ya sake jaddada aniyarsa ta yin dukkanin abin da za ta iya wajen ƙarfafa kayayyakin cikin gida da dogaro da kai da kuma fada da rashawa da cin hanci da kuma nuna wariya yana mai cewa gwamnatinsa za ta kasance gwamnati ce da dukkanin al’ummar Iran.

342/