Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

24 Yuli 2021

06:26:27
1162647

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Yi Alluran Riga Kafin Cutar Covid19 Karo Na Biyu A Yau Jumma’a

A safiyar yau jumma’a ce jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran, Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamina’I ya yi alluran riga kafin cutar Covid 19 karo biyu kuma kirar cikin gida mai suna Coviran-Barakat.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Jagoran ya yi alluran riga kafin cutar ta Covid 19 a karon farko ne a ranar 25 ga watan Yunin da ya gabata.

Labarin ya kara da cewa bayan yin alluran, jagoran ya bukaci masana a cikin kasar su yi iyakar kokarinsu na ganin sun wadatar da kasar da alluran ta yadda ba za ta bukaci shigo da ita daga kasashen waje ba.

A halin yanzu dai an fara samar da alluran a cikin gida, amma saboda ana bukatar gaggauta yiwa mutanen kasar alluran riga kafin, ana shigo da amintattun daga cikinsu daga kasashen waje.

Kasar Iran dai ta na daga cikin kasashen wadanda suke da fasahar samar da alluran riga kafin cutar ta Covid 19 A duniya guda 6. Wato bayan Amurka, Ingila, India, Cana da Rasha.

Dangane da karancin ruwa da ake fama da shi a lardin Khuzitan kuma, wanda labarin ya game kafafen yada labarai na duniya, musamman na makiya, jagoran yayi kira da jami’an gwamnatin klasar su gaggauta magance matsalar.

342/