Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

29 Mayu 2021

14:14:51
1145488

​Iran: Janar Qa’ani Ya Ba Wa Yahudawan Sahyoniyya Shawarar Barin Kasar Falasdinu Da Gaggawa

Gwamandan rundunar Qudus ta dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran Janar Qa’ani yay i kira ga yahudawan sayhoniyya a kasar Falasdinu da su gaggauta komawa gidajensu a turai da Amurka kafin su kara da tsada.

ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka a safiyar yau a lokacinda yake halattan taron hatamar 40 da rasuwar Janar Sayyeed Mohammad ijazee a nan Tehran.

Qa’ani ya kara da cewa a matsayina na wanda ya san dakaru masy gwagwarmaya a kasar Falasdinu, lokacin ya wuce kuma, na yahudawan su durkusar da dakarun Falasdinawa da bindigogi da kuma kannana makamai.

Kwamanda ya kammala da cewa dukkan makamai masu linzami fiye da 3000 wadanda dakarun falasdinawa suka cillan kan yahudawan Sahyoniyya kirarsu ne a cikin gida. Ya ce yayi imani gwamnatin mamaya ta HKI ta zo karshe kuma bata da zaben kowama inda suka fito daga Amurka da klasashen Turai.

342/