(ABNA24.com) Harin na farko an kai shi ne da rokoki kan yankin nan mai cikakken tsaro da ake kira ‘’Green zone’’ dake Bagadaza babban birnin kasar wanda ya kunshi ma’aikatun diflomatiyya ciki har da ginin ofishin jankadancin Amurka.
Sai kuma na biyu wanda aka kai kan sansanin sojin saman Iraki na Balad wanda ya kunshi sojoji da jiragen saman Amurka.
Wata sanarwa da rundinar sojin Iraki ta fitar ta ce, ba a rasa rai ba ko jikkata a hare haren.
Bayan hakan dai rundinar sa kai ta ‘’Hachd al-Chaabi’’ ta bukaci jami’an tsaron Iraki dasu nisanci sansanin da kimanin kilomita guda, daga karfe biyar agogon wurin (14:00 GMT) daga yau Lahadi.
A wani lokaci yau Lahadi ne ake sa ran majalisar dokokin Iraki, za ta gudanar da wani taron gaggawa, wanda a yayinsa ake tsammanin za’a kada kuria’r korar sojojin Amurka 5,200 dake jibge a kasar.
/129
6 Janairu 2020 - 05:46
Lambar labari: 999721
A Iraki, an kai jerin hare hare biyu kan sansanonin sojin Amurka da yammacin Asabar.