(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rauhani ya ziyarci gidan shahid Janar Sulaimani a jiya Juma’a don gabatar da ta’aziyya ga iyalan gidansa wadanda suka hada da matarsa da kuma yayansa.
A daren juma’ar da ta gabata ce sojojin Amurka a kasar Iraqi suka kai hari kan tawagar motoci dauke da Janar Sulaimani da Mahadi Muhandes da tawagarsu a kusa da tashar jiragen saman na Bagdaza wanda ya yi sanadiyar shahadarsu.
A yau ne ake juyayin shahadarsu a kasar ta Iraqi kafin a kawo Shahid Sulaimani kasar Iran.
Gwamnatin kasar Iraqi dai ta yi tir da hare-haren a yayinda kasar Iran ta ce za ta dauki fansa a lokacin da ya dace.
/129
5 Janairu 2020 - 04:59
Lambar labari: 999347
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rauhani ya ziyarci gidan shahid Janar Sulaimani a jiya Juma’a don gabatar da ta’aziyya ga iyalan gidansa wadanda suka hada da matarsa da kuma yayansa.