(ABNA24.com) ‘Yan Sanda Sun Bude Wuta Tare Da Kashe Mutum 1 a cikin masu zanga zangar neman sakin Sheihk Zakzaky A Sokoto.
An bayyana sunan mutumin da aka kashe a ranar Juma’a da sunan Yahuza Umar Kalabaina.
Bayanai sun ce yan sanda sun harbe Yahuza din ne kai tsaye a ka.
Ko baya ga hakan da akwai mutane da dama da suka jikkata a lokacin da ‘yan sanda ska bude musu wuta, a zanga zangar lumanar da suke ta neman a saki Sheikh Zakzaky da hukumomnin kasar ke tsare da.
Rahotanni sun ce an kori jama’a
dake daukan hoto a lokacin da ‘yan sanda ke murkushe masu zanga zangar.
Tun a cikin shekara 2015 ne aka tsare da Sheikh Zakzaky, da mai dakinsa Zainat, bayan harin da sojoji suka kai masu a garin Zaria, inda kuma aka kashe masa mabiya kimanin 1,000.
/129
29 Disamba 2019 - 07:28
Lambar labari: 997177
‘Yan Sanda Sun Bude Wuta Tare Da Kashe Mutum 1 a cikin masu zanga zangar neman sakin Sheihk Zakzaky A Sokoto.