11 Disamba 2019 - 05:54
Iran Ta Bukaci 'Yan Kasarta Su Dakatar Da Zuwa Faransa

A yayin da yajin aiki ke kara kamari a kasar Faransa, ma'aikatar harakokin wajen Iran ta bukaci 'yan kasar dake son yin bulaguro zuwa kasar Faransa da su dakatar.

(ABNA24.com) A yayin da yajin aiki ke kara kamari a kasar Faransa, ma'aikatar harakokin wajen Iran ta bukaci 'yan kasar dake son yin bulaguro zuwa kasar Faransa da su dakatar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar da jiya talata, ma'aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ta bukaci 'yan kasar dake niyar bulguro zuwa kasar Faransa su dakatar domin kare lafiyarsu.

A cikin wannan shekara, kasar Faransa ta fuskanci zanga-zanga da yajin aiki da dama na nuna adawa da matakin sauye-sauyen da shugaban kasar Faransa ke son aiwatarwa a kasar, a cikin 'yan makonin nan zanga-zangar da yajin aikin sun fi kamari , inda rahotani ke cewa kashi 80% na ma'aikatan kasar na cikin yajin aiki.

A halin yanzu kuma, babu alamar wannan zanga-zanga za ta kawo karshe, lura da cewa kwanaki shida kenan da masu boren ke fantsama kan tituna.

Zanga-zangar ta fi kamari a birnin Paris, inda akalla kashi 35 na malaman makarantun boko suka kaurace wa ayyukansu kamar yadda Ministan Ilimi Jean Michel Blanquer ya sanar.

Kazalika, bangaren sufuri a birnin na Paris na ci gaba da kasancewa a durkushe, lura da cewa, hanyoyin jiragen kasa guda biyu kadai ne ke aiki kamar yadda aka saba , yayin da aka rufe sauran hanyoyin, kana aka soke zirga-zigar jiragen sama da dama.

Ana kallon wannan boren a matsayin mafi muni da Kungiyar Kwadagon Faransa ta shirya tun bayan darewar shugaba Macron kan karagar mulki a shekarar 2017, inda ya yi alkawarin inganta tattalin arzikin kasar.


/129