9 Disamba 2019 - 06:45
Ana Ci gaba Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Nigeria Game Da Shaikh Zakzaky

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Musawi sa’ilin da yake amsa tambayoyin Yan jaridu game da halin da jagoran yan uwa musulmi a Nigeria Shaikh Ibrahim Elzakzaky yake ciki,

(ABNA24.com) Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Musawi sa’ilin da yake amsa tambayoyin Yan jaridu game da halin da jagoran yan uwa musulmi a Nigeria Shaikh Ibrahim Elzakzaky yake ciki, ya bayyana cewa bisa la’akari da ganawa da aka yi tsakanin shugaban Nigeria Mohammadu Buhari da mataimakin shugaban Iran kan tattalin arziki Dr Nahabandiyan sun tattauna game da abubuwa daban -daban ciki har da batun sheikh zakzaky , wanda haka ya bada damar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu akan yadda za’a bi hanyoyin diplomasiya domin ganin cewa Iran ta taimaka wajen kawo karshen matsalar.

Hakazalika Ya fadi cewa yana fatan ci gaba da tattaunawar da ake yi da gwamnatin Nigeria zai taimaka sosai wajen ganin an warware matsalar cikin gaggawa,

Shi dai mataimakin shugaban kasar Iran Nahbandiyan ya gana da shugaban Buhari na Nigeria ne a bayan taron kungiyar shuwagabannin kasashe masu fitar da iskar gas (OPEC) ne da aka yi a birnin Malabo na kasar Guinea Bissau,



/129