7 Disamba 2019 - 04:54
Za’a Bukaci Kotun ICJ Da Ta Dakatar Da Cin Zarafin Musulman Rohingya A Myammar

Kasar Gambiya ta sanar da cewa za ta bukaci Kotun Duniya da ke birnin Haque da ta dau matakan da suka dace wajen hana gwamnatin kasar Myammar ci gaba da cin zarafi al’ummar Musulmin kasar da ake yi.

(ABNA24.com) Kasar Gambiya ta sanar da cewa za ta bukaci Kotun Duniya da ke birnin Haque da ta dau matakan da suka dace wajen hana gwamnatin kasar Myammar ci gaba da cin zarafi al’ummar Musulmin kasar da ake yi.

Tun da fari dai gwamnatin kasar Gambiyan ce ta shigar da wannan kasar a gaban kotun saboda irin kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar musulmi na Myammar din, to sai dai da yake har yanzu ba a fara shari’ar ba, shi ne ta sanar da cewa za ta bukaci kotun da ta umurci gwamnatin Myammar din da ta dakatar da wannan danyen aikin kafin a ma fara asalin shari’ar.

Rahotanni sun ce a ranar 10 ga watan Disamba din nan ne za a shiga da bukatar ga majalisar alkalan kotun wacce take a matsayin wata cibiya ta Majalisar Dinkin Duniya mai shiga tsakanin kasashe.

Shekara da shekaru kenan al’ummar Musulmin Rohingya su ke fuskantar musgunawa da kuma kisan kiyashi daga sojojin gwamnati da sauran mabiya addinin Buddha masu tsaurin ra’ayi lamarin da hatta MDD ta yi Allah da shi.



/129