(ABNA24.com) Mataimakin kungiyar gwagwarmayar kasar Iraki ta Hashadu-sha'abi Abu Mahadi Al-Muhandis ya ce dakarun kungiyar suna cikin shirin ko ta kwata a dukkanin jihohin kasar domin kalubalantar barazanar kungiyar ISIS tare da tabbatar da cewa dukkanin kwamandojin kungiyar sune sahun gaba da fagen daga domin kare kasarsu daga duk wata barazana ta makiyan kasar Iraki.
Abu Mahadi ya ce za su dauki duk matakin da ya dace na ganin cewa kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ba ta sake zama barazana ga kasar Iraki ba.
A marecen jiya Talata, rundunar tsaro ta 44 ta kungiyar Hashadu Sha'abi ta samu nasarar dakile wani harin ta'addanci da mayakan 'yan ta'addar ISIS suka kai a yankin Al-khadar dake kudancin garin Mosil.
Sanarwar ta ce manufar 'yan ta'adda samar da rashin tsaro a kauyuka da lardunan kudancin jihar Nainuwa da arewa maso yammacin jihar jihar salahuddin da kuma rufe hanyoyin wadannan yankuna.
/129
5 Disamba 2019 - 08:24
Lambar labari: 991591
Kungiyar gwagwarmayar kasar Iraki Hashadu-Sha'abi ta sanar da cewa bisa alkawarin da suka dauka na kare kasa ba za su sake bari kungiyar ISIS ta dawo ta hargitsa harakokin tsaron kasar ba