4 Disamba 2019 - 04:26
 Larijani: Ta Hanyar Tattauna Ne Kadai Za A Iya Warware Rikicin Kasar Yemen

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da ministan harkokin wajen kasar Oman da ya ke ziyarar aiki a nan Iran.

(ABNA24.com) Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da ministan harkokin wajen kasar Oman da ya ke ziyarar aiki a nan Iran.

Wani sashe na kalaman Dr. Ali Larijani sun kunshi cewa; Batun Samar da zaman lafiya a kasar Yemen, yana da matukar muhimmanci a wurinmu, kuma lokaci ya yi da daya bangaren zai fahimci cewa; Ba zai iya warware matsalar kasar ta Yemen da karfi ba, wajibi ne a matakin farko a tsagaita wuta sannan kuma a bude tattaunawa akan yadda za a magance rikicin daga tushensa.

Danage da alakar Amurka da Iran kuwa, Ali Larijani ya ce; Al’umma ta fahimci cewa Trump yana gaba da Iran, kuma babu hikima a cikin halayyar Amurka.

Dr. Ali Larijani ya kuma ce; Rawar da kasar Oman take takawa domin tabbatar da zaman lafiya a cikin wannan yankin abu ne mai jan hankali matuka.

Har ila yau, Dr. Ali Larijani ya yi ishara da kyakkyawar alakar da take tsakanin Iran da Oman, yana mai cewa; A kodayaushe alakar kasashen biyu tana sake bunkasa.



/129