12 Nuwamba 2019 - 05:12
Ministan Harkokin Wajen Kasar Rasha Ya ce; Dole Ne Sojojin Syria Su Shimfida Ikonsu A Dukkanin Fadin Kasar

Ministan harkokin wajen na kasar Rasha ya kuma kara da cewa; Kasarsa za ta tabbatar da cewa gwamnatin Syria ta sake shimfida ikonta akan dukkanin kasar daga ciki hadda rijiyoyin man fetur din da Amurka ta mamaye.

(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen na kasar Rasha ya kuma kara da cewa; Kasarsa za ta tabbatar da cewa gwamnatin Syria ta sake shimfida ikonta akan dukkanin kasar daga ciki hadda rijiyoyin man fetur din da Amurka ta mamaye.

Ministan harkokin wajen na kasar Rasha wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya kuma ce; Shimfida ikon gwamnatin Syria ne a fadin kasar zai kawo karshen ta’addanci ya kuma kawo karshen matsalolin siyasar kasar.

A cikin kwanakin bayan nan ne dai aka bayyana cewa sojojin Amurka sun kai motocin yaki da tankoki a yankin da rijiyoyin man fetur din kasar ta Syria su ke.

Tun da fari shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa; Sojojin kasarsa sun kafa sansani yankin gabashin kasar ta Syria da ke da rijiyoyin man fetur saboda kare su daga “Da’esh’ kamar yadda ya bayyana.





/129