(ABNA24.com) Babban sakatare janar din kungiyar Hisbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hasssan Nasrullaha yayin tarongirmama babban malamain addinin Musulunci a kasar, Allama Sayyid Ja’afar Murtadha da Allah ya yi wa rasuwa, ya fadi cewa; Makiya na kashe makuden kudade wajen murguda bakutun dayasa jama’a suka fito Zanga- zanga, don haka muke kokari wajen ganin kasar ba ta fada cikin rikici da rashin tabbas ba, kuma Hizbulla ba tana neman mulki ido rufe ba ne.
Har il yauya kara da cewa bayan kwashe makwanni biyu ana Zanga- zanga a kasarda kuma abubuwan da suka biyo baya, rahotanni da muka samu sun tabbatar da cewa ko shakka babu akwaimasu kulla makircin ganin sun jefa kasar cikin yakin basasa, inda suka rika yada kalaman tunzira jama’ada cin zarafin wasu fitattun mutane a kasar, inda wasu suka shiga rigar masu Zanga - zangadomin yin amfani daadawar siyasa da nufin durkusar da harkokin siyasar Kasar baki daya.
Daga karshe Sayyid Nasrullah ya bukaci a koma teburin tattaunawa tsakanin bangarorin siyasar kasar domin samun maslaha, kana ya tabbar da cewa Amurka na da hannuwajen ganin ba’a kai ga cimma matsayar da za ta taimaka wajen ganin kasar ta fita daga halin tsaka mai wuya da take ciki.
/129
2 Nuwamba 2019 - 06:38
Lambar labari: 985529
Babban sakatare janar din kungiyar Hisbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hasssan Nasrullaha yayin tarongirmama babban malamain addinin Musulunci a kasar, Allama Sayyid Ja’afar Murtadha da Allah ya yi wa rasuwa, ya fadi cewa; Makiya na kashe makuden kudade wajen murguda bakutun dayasa jama’a suka fito Zanga- zanga, don haka muke kokari wajen ganin kasar ba ta fada cikin rikici da rashin tabbas ba, kuma Hizbulla ba tana neman mulki ido rufe ba ne.