24 Oktoba 2019 - 06:35
An Fara Taron Ministoci Na Kungiyar Yan Baruwammu A Birnin Baku

A yau ne aka fara taron ministoci harkokin waje na kungiyar kasashen ‘yan ba ruwammu ko (NAM ) a birnin Baku babban birnin kasar Azerbaijan.

(ABNA24.com) A yau ne aka fara taron ministoci harkokin waje na kungiyar kasashen ‘yan ba ruwammu ko (NAM ) a birnin Baku babban birnin kasar Azerbaijan.

Kamfanin dillancin labaran “Iran Press” ya bayya cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Dr Muhammad Jawad Zareef yana daga cikin ministocin da suke halattan taron. Sannan ajawabin da ya gabatar, a yau Laraba, Zarif ya yi allawadai da ta’addancin tattalin arziki wanda gwamnatin kasar Amurka take dorawa wasu kasashen duniya, sannan ya bukacikasashen duniya su dauki matsayi guda don fuskatar ayyukan ta’addancin na kasar ta Amurka.

A yau da gobe ne ake saran ministocin zasu kammala ayyukan sharar fage na taron shuwagabannin kungiyar ta NAM na kwanaki biyu, wato daga ranar jumma’a 25-26 na wannan watann da muke ciki.

Wakilan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 158 ne zasu halarci taron na Baku, sannan shuwagabannin kasashen kungiyar da kuma shuwagabannin gwamnatoci 101 zasu halarci taron a wannan karon. Kasar Azerbaijan ce ta karbi bakonci da kuma shugabancin kungiyar a wannan karon.



/129