(ABNA24.com) An yi taho mu gama tsakanin magoya bayan jam’iyyun adawa da kuma jami’an tsaro a kasar Guinea, a daidai lokacin da magioya bayan jam’iyyun adawar suke gudanar ad zanga-zangar nuna kin amincewa da abin da suka kira yunkurin shugaba na neman ta zarce.
Wasu bayanai daga Ma'aikatan lafiya a Guinea sun ce an kashe a kalla mutum biyu a yayin gudanar da wanann zanga-zanga, wasu da dama kuma sun samu munanan raunuka.
Jami'an tsaron kasar ta Guinea sun yi amfani da harsasai na gaske da gurnati mai gigitawa da kuma hayaki mai sa hawaye a kokarin da suke yi na kawar da masu zanga-zangar.
Masu zamga-zamgar dai sun dai kafa shingaye kuma sun rika kona tayoyi a yayin da suka rika jifan jami'an tsaro da duwatsu. Tuni dai aka kulle makarantu da shaguna da kasuwanni a babban birnin kasar, yayin da jami’an tsaro suke ta sintiri, haka nan kuma an wasu tarin jami’an tsaro sun killace gidajen wasu jagorin yan adawar.
Shugaba Apha Conde wa’adinsa na biyu zai kare ashekara mai zuwa, wamda kuma ba shi da hurumin sake tsayawa wata takara idan wa’adinsa ya kare bisa ga dokar kundin tsarin mulkin kasar, amma ga dukkanin alamu yana neman yin ta zarce, inda ya bukaci da a yi nazari kan samar da wata doka wadda za ta ba shi damar zarcewa, tare da neman a gudanar da kuri’ar raba gardama kan hakan.
/129