(ABNA24.com) A Burkina Faso, mutane kimanin ashirin ne suka rasa rayukansu, a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani wajen hakar zinari dake yankin Dolmane dake karamar hukumar Arbinda a arewacin kasar.
Bayanai daga kasar sun ce akasarin wadanda lamarin ya rusa dasu masu hakar zinari ne a yankin.
Ba’a dai fayyace ko suwa ne ke da alhakin harin ba, amma an ce a yankin ne wasu mayakan dake ikirari da sunan jihadi suka ruguza wata gadada abubuwa masu fashewa a tsakiyar watan Satumba a kusa da garin Arbinda, kana hanyar zuwa yankin Djibo.
Yau kusan shekaru hudu kenan da kasar Burkina Faso, dake yankin Sahel, ke fuskantar hare hare da ake dangantawa da na mayakan dake ikirarida sunan jihadi, wadanda suka hada da rassan Al-Qaida da kuma kungiyar IS, hare haren da kawo yanzu suka yi sanadin mutuwar mutane 600 a yankin arewa maso gabashin kasar a alkalumman da lamfanin dilancin labaren AFP ya fitar.
/129
7 Oktoba 2019 - 05:35
Lambar labari: 980774
A Burkina Faso, mutane kimanin ashirin ne suka rasa rayukansu, a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani wajen hakar zinari dake yankin Dolmane dake karamar hukumar Arbinda a arewacin kasar.