6 Oktoba 2019 - 06:03
​Kudin Rial Na Iran Ya Sake Farfadowa Duk Da Takunkumin Amurka

Gwamnan babban bankin kasar Iran ya bayyana cewa, kudin kasar sun sake farfadowa, duk kuwa da takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta kakaba wa kasar.

(ABNA24.com) Gwamnan babban bankin kasar Iran ya bayyana cewa, kudin kasar sun sake farfadowa, duk kuwa da takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta kakaba wa kasar.

A lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran IRNA a yau, Abdulnasir Himmati gwamnan babban bankin kasar Iran ya bayyana cewa, a halin yanzu darajar kudin kasar na sake farfadowa, bayan kimarsu ta yi kasa a ‘yan watanni baya, sakamakon takunkumin Amurka.

Ya ce ahalin yanzu kimar kudin rial na Iran ta karu da kimanin kashi 40%, idan aka kwatanta da ‘yan watanni baya, kuma kullum kimar kudin na karuwa sakamakon matakan da babban bankin kasar ya dauka, domin tunkarar faduwar darajar kudin kasar.

Haka nan kuma ya yi ishara da wasu matakan da suke shirin dauka, wanda za su kara dawo da darajar kudin kasar nan da wasu ‘yan lokuta masu zuwa, wanda hakan zai kara karfafa tattalin arzikin kasar.

Kasar Iran dai ita ce kasa ta hudu a duniya wajen yawan danyen man fetur, wanda kuma yana daya daga cikin hanyoyinta na samun kudaden shiga, amma sakamakon matsin lambar Amurka, da kuma takunkuman da ta dorawa kasar ta Iran, hakan ya sanya Iran ta mayar da hankali a kan wasu abubuwa da take samarwa, maimakon dogaro da danyen amn fetur.




/129