(ABNA24.com) Bayan tashe-tashen hankulan da suka wakana a birnin bagadaza na kasar Iraki da ma wasu biranan yankin kudancin kasar, kura ta lafa a birnin bagadaza wasu yankuna da dama.
Kamfanin dillancin labaran Saumariyya News ya bayar da rahoton cewa, an janye dokar hana zirga-zirga a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, da ma wasu biranan da aka yi fama rikici kwanaki biyu da suka gabata.
Rahoton ya ce a yau shugaban kasar at Iraki Barham Saleh tare da firayi minister Adel Abdulmahdi sun gudanar da wata tattaunawa danagne da abubuwan da suka wakana, domin daukar matakai na gaba wajen ci gaba da daidaita lamurra a kasar.
A daya bangaren kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Iraki a yau ya gana da wakilan masu gudanar da zanga-zanga, domin tatatunawa kan bukatunsu tare da ‘yan majalisa, tare da tabbatar musu da cewa suna hakkin su yi zanga-zangar lumana domin bayyana korafe-korafensu.
Tun a farkon wannan watan ne wata zanga-zanga ta barke a wasu biranan kasar Iraki, domin nuna damuwa kan matsalolin da ake fama da su, musamamn ma rashin ayyuka a tsakanin matasa, inda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka kona kaddarorin gwamnati da kuma na jama’a, lamarin da yasa jami’an tsaro suka dauki matakin tarwatsa su.
/129