26 Satumba 2019 - 04:28
Pakistan : Mutane 22 sun mutu a girgizar kasa

A Pakistan wata girgizar kasa data abkawa kasar ta yi sanadin mutuwar mutane 22 , da kuma haddasa barna mai yawa.

(ABNA24.com) A Pakistan wata girgizar kasa data abkawa kasar ta yi sanadin mutuwar mutane 22 , da kuma haddasa barna mai yawa.

Ko baya ga hakan hukumomin kasar sun ce akwai daruruwan mutane da suka raunana ta hanyar karaya da kuma raunuka ka, a girgizar kasar mai karfin maki 5,2 a ma’aunin girgizar kasa.

Jami’an agaji sun kwashe daren jiya suna aiki ceto, a yayin da ake garzayawa da wadanda suka raunana a asibitin yankin.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin hanyoyi da gadoji da gidaje da dama sun lalace.

Ruwan sama da ake samu a yankin na iya kawo cikas wajen gudanar da ayyukan ceto.




/129