(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen na kasar Iran ya fadi hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin yan jarida a wajen taron kasa da kasa game da batun hadarin yaki da makomar tekun fasha, ya kara da cewakasar birtaniya ta tsare jirgin ruwan dakon man kasar Iran duk da yake cewa ba kasar siriya sai je ba,kuma ba laifi ba ne Iran ta siyar da man fetur dinta, don haka hanya daya tilo itace mutunta dokokin kasa da kasa ,Iran tana da karfi sosai a tekun fashadon haka samar da zaman lafiya a tekun fasha da mashigar ruwa ta Hurmuz ba zai ta ba yiyuwa ba tara da Iran a ciki ba.
Har iya yau ya kara da cewa Amura tana neman rikici ne kawai a yankinmu amma mu mun nunawa duniya cewa muna son tattaunawa ,mun kwashe shekaru 2 muna tattaunawa an cimma matsaya amma daga karshe Amurka ta fice daga yarjejeniyar, kuma ta kakabawa Iran takunkumitattalin arziki mafi tsananin, da zai shafi mutanen gari kai tsaye.
Daga karshe ya nuna cewa mu ba zamu fara yaki da wata kasa ba, kuma bamu kai hari akan kowa ba, don haka afili yake cewa tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tekun fasha zai samu ne ta hanyar yin aiki tare da tsakanin kasashen yankin ba tare da stoma bakin yan babakere ba.
/129