18 Agusta 2019 - 09:54
Iran Za Ta Fara Kera Injinan Jiragen Sama Daban-Daban

Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Major General Muhammad Bakiri ne ya bayyana cewa; Nan da wani lokaci kadan Iran za ta fara kera injina daban-daban na jiragen sama da kuma na jirage masu saukar angulu.

(ABNA24.com) Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Major General Muhammad Bakiri ne ya bayyana cewa; Nan da wani lokaci kadan Iran za ta fara kera injina daban-daban na jiragen sama da kuma na jirage masu saukar angulu.

Major General Bakiri wanda ya kai ziyara a wurin baje kolin kere-keren soja a yau Asabar, ya kara da cewa; tare da takunkuman da aka kakabawa Iran masu tsanani wadanda su ka fara tun cin nasarar juyin musulunci, musamman a fagen harkokin tsaro, sai dai duk da hakan, ci gaban da Iran take samu bai taba tsayawa ba.

Babban hafsan hafsoshin sojan na Iran ya kuma ce; Kokarin da Iran din take yi na zama mai cin gashin kanta ta fuskar tsaro da kuma bunkasa kwarewar da take da ita, suna nuni ne da muhimmancin da aikin da sojojin kasar suke yi.

Major General Bakiri ya kuma ce; Bangaren tsaro na kasa yana daga cikin bangare mafi muhimmanci na ci gaban, kuma tuni ministan tsaro ya bayyana cewa a shirye suke su warare duk wata matsala da ake fuskanta.


/129