5 Agusta 2019 - 07:19
​Larijani: Kakaba Takunkumin Kan Zarif Ya Tabbatar Da Munafuncin Siyasar Amurka

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa, kakaba takunkumin da Amurka ta yi a kan ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif, hakan ya tabbatar da munafuncin siyasar Amurka.

(ABNA24.com) Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa, kakaba takunkumin da Amurka ta yi a kan ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif, hakan ya tabbatar da munafuncin siyasar Amurka.

Tashar Presstv ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Afghanistan Fazl Hadi Moslem Yar a jiya a birnin Tehran, shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa, babu gaskiya a da’awar da Amurka take yin a neman tattaunawa da kasar Iran.

Larijani ya kara da cewa, saka takunkumi kan Zarif, ya kara tabbatar da cewa Amurka ba da gaske take yi ba, domin kuwa Zarif shi ne babban jami’in diflomasiyyar kasar Iran, wanda kuma shi ne ke jagorantar duk wata tattaunawa tsakanin kasar da sauran manyan kasashen duniya.

Amurka dai ta bayyana cewa, ta saka wa Zarif takunkumi ne sakamakon yadda yake yin magana a madadin jagoran juyin juyin hali na kasar Iran, yayin da sauran kasashen duniya daga ciki har da manyan kawayen Amurka na turai, suka yi watsi da wannan mataki.



/129