31 Yuli 2019 - 04:01
​Zarif: Iran Ba Zata Amince Da Rasa Ko Da Taki Guda Daga Kasarta Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa ma’aikatarsa ba zata taba amincewa da rasa ko da taki guda na kasar, ga duk wata kasa daga kasashen da suke makobtaka da kasar ba.

(ABNA24.com) Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zarif yana fadar haka a safiyar yau Talata, a gaban ‘yan majalisar dokokin kasar a nan Birnin Tehran.

Ministan ya kara da cewa tun bayan faduwar tarayyar Soviet a shekara 1991 ma’aikatar harkokin wajen kasar take kokarin ganin kasar bata rasa ko da kafa guda na yankinta ga kasashe makobta ba, musamman a yankin tekun casbiyan,inda kasashe biyar suke makobtaka da shi.

Zarif ya kara da cewa ma’aikatarsa ta shaidawa dukkan kasashen da suke makobtatakam da tekun Caspian kan cewa kada su yanke wata shawara danagen da ruwa da kuma arzikin da ke cikin tekun ba tare da halartan kasar Iran ba.

Daga karshe Zarif ya kammala da cewa, kafin nasarar juyin juya halin musulunci a kasar ta Iran a shekara ta 1979, sarakunan kasar sun yi ta bada wasu yankunan kasar ga wasu kasashe ko kuma basu ‘yenci.

Amma bayan nasarar juyin juya halin musulunci shekaru 40 da suka gabata, kasar bata rasa ko da taki guda daga cikin yankunan kasar ba.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin kasar ta Rashan ta fara gabatar da shawarar gudanar da taro ta kasa da kasa kan harkokin tsaro a yankin tekun farisa, da kuma kafa kungiya ta tabbatar da tsaro a yankin wanda yake da muhimmanci ga kasashen duniya da dama.

/129

​Zarif: Iran Ba Zata Amince Da Rasa Ko Da Taki Guda Daga Kasarta Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa ma’aikatarsa ba zata taba amincewa da rasa ko da taki guda na kasar, ga duk wata kasa daga kasashen da suke makobtaka da kasar ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zarif yana fadar haka a safiyar yau Talata, a gaban ‘yan majalisar dokokin kasar a nan Birnin Tehran.