29 Yuli 2019 - 04:01
Sudan : Za’a Hukunta Sojojin Da Suka kashe Masu Zaman Dirshin

Kotu a Sudan, ta bayyana cewa za’a hukunta wasu jami’an soji guda takwas bisa cin zarafin bil adama, biyo bayan mutuwar masu zanga zanga a ranar 3 ga watan Yuni da ya gabata.

(ABNA24.com) Kotu a Sudan, ta bayyana cewa za’a hukunta wasu jami’an soji guda takwas bisa cin zarafin bil adama, biyo bayan mutuwar masu zanga zanga a ranar 3 ga watan Yuni da ya gabata.

Shugaban kwamitin binciken kisan da akayi a ranar 3 ga watan Yunin, Fath al-Rahman Saeed, ya bayyana cewa mutane 87 ne aka kashe, kana wasu 68 suka jikkata a yayin da sojojin sukayi amfani da karfi wajen murkushe masu zaman dirshin din gaban hedikwatar sojojin kasar a Khartoum.

Saidai likitocin dake da kusanci da masu zanga zangar sun ce mutane 130 ne sojojin suka kashe a ranar 3 ga watan Yunin.

Wasu bayanai sun ce akwai mutane dayewa da aka jefa a cikin tafkinNilu da ya ratsa birnin Kharoum.



/129