27 Yuli 2019 - 06:53
Janar Salami: Babu Wani Jrgin Iran Maras Matuki Da Ya Fadi

A yayin da yake ziyara Lardin Lorestan a jiya Laraba, babban kwamandan dakarun kare juyin musulunci a Iran janar Salami ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani jirgi maras matuki mallakin kasar Iran da aka kakkabo ko kuma ya fadi da kansa saboda wata matsala.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, a jiya Llaraba babban kwamandan rundunar IRGC Janar Salami ya bayyana wa 'yan jaridu cewa ya zuwa yanzu babu wani jirgin maras matuki mallakin kasar da ya fadi , idan kuma makiya kamar yadda suka yi su nada hujja, to sai su bayyanata, domin mu mun bayyana tamu hujjar, ta hanyar nuna wa al'ummar Iran da Duniya yadda jirginmu maras matuki yayi shawagi na tsahon sa'o'i uku da minti 40, ya kuma dauko hotutan duk jiragen ruwa na dakon man da suke wuce ta mashigar Hurmuz a wannan lokaci.

Salami ya kara da cewa A yau babu wata kasa da zata fitar da wata magana ba tare da ta gabbatar da hujja ba, don haka idan makiya nada hujjar yadda suka harbo jirgi maras matuki na kasarmu to su gabatar, don haka muta tabbatar muku da cewa abin da makiya suka fada ba gaskiya ba ne, kuma mun tabbatarwa Duniya hakan.




/129